Friday, 14 February 2020
Ajax ta sayar wa da Chelsea Hakim Ziyech

Home Ajax ta sayar wa da Chelsea Hakim Ziyech
Ku Tura A Social Media


Ajax ta amince ta sayar wa da Chelsea dan wasa Hakim Ziyech kan sama da fam miliyan 33 a bana.

Mai shekara 26, yana daga cikin 'yan kwallon da Lampard ya so ya buga wa Chelsea tamaula a Janairun nan.
Ajax ta tabbatar cewar ta amince ta sayar da dan kwallon kan fam miliyan 33.3 zai iya kai wa fam miliyan 36.3 da zarar Ziyech ya amince da kunshin yarjejeniya.

Sai dai kuma Ajax ce ba ta sayar wa da Chelsea dan wasan ba, ganin tana fatan lashe kofin kasar Netherlands a bana.
Dan wasan na tawagar Morocco shi ne zai zama na farko da Lampard zai kai Chelsea, tun bayan da aka amince ta sayi 'yan kwallo.

A baya ne hukumar kwallon kafa ta duniya, FIFA ta dakatar da Chelsea daga sayen 'yan kwallo, bayan da aka sameta da laifin karya ka'idar sayen matasan 'yan wasa.

An alakanta Chelsea da sayen 'yan wasa da dama a watan Janairu ciki har da dan kwallon Paris St-Germain, Edinson Cavani da na Napoli, Dries Mertens.

Lampard ya fuskanci dalilin da ya sa suka kasa sayen 'yan kwallo a Janairu da ya hada cewar kungiyoyi ne suka ki amincewa su sayar, ba laifin masu sayo 'yan wasa a Chelsea ba ne.

Ziyech yana daga cikin wadan da suka ci wa Ajax kwallo a wasan da suka tashi da Chelsea 4-4 a Champions League a cikin watan Nuwamba.

Share this


Author: verified_user

0 komentar: