Tuesday, 11 February 2020
Atiku Yayi lale Marhabin Da Samun Daktoci Mata Guda Biyar A Jahar Sa 'Yan Gida Daya

Home Atiku Yayi lale Marhabin Da Samun Daktoci Mata Guda Biyar A Jahar Sa 'Yan Gida Daya
Ku Tura A Social Media

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar, ya jinjina wa wasu mata likitoci ‘yan gida daya.

Daya daga cikinsu ne ta wallafa hotonsu su biyar inda ta ce mahaifinsu guda kuma dukkansu likitoci ne da suka kware a fannoni daban-daban.

Da yake tsokaci a kan hoton, dan takarar shugabancin kasar a karkashin jam’iyyar PDP a zaben 2019, ya ce babu abin da ya fi dacewa ga al'umma fiye da bai wa mace ilimi.

“Abin sha’awa ne. Idan ka bai wa mace ilimi, ka ilimantar da iyali da ma al’umma ne,” in ji Atiku.

Share this


Author: verified_user

0 komentar: