Friday, 14 February 2020
Na yadda cewa akwai Allah, amma ban yadda akwai Wuta da Aljannah ba

Home Na yadda cewa akwai Allah, amma ban yadda akwai Wuta da Aljannah ba
Ku Tura A Social Media
Fitacciyar jaruma ‘yar kasar Ghana, Efia Odo ta karyata imanin da Kiristoci suke da shi na cewa akwai wuta da aljannah.

Kasar Ghana dai akasari kasa ce ta Kiristoci, inda ‘yan kasar da yawa suka yadda cewa akwai wuta da aljannah, kuma suke muradin idan sun mutu za su shiga aljannah yayin da suke kuma addu’ar ganin makiyansu a wuta.

Yiwa makiyi addu’ar Allah ya sanya shi a wutar Jahannama yana daya daga cikin tsohuwar al’adar mutanen kasar Ghana, duk kuwa da cewa Allah ya ce ka so makiyinka ko ya yake.

Koma dai yane dai, Efia Odo, wacce ta nuna rashin yardarta akan wannan magana, inda ta karyata zancen cewa akwai wuta da aljannah.

A cewar ta, ita ta yadda akwai Allah, amma ba ta yadda akwai wuta da aljannah ba.
Jarumar fim din tayi rubutu a shafinta na Twitter kamar haka: “Na yadda akwai Allah. Amma wuta da aljannah ba wurare bane a wajena. Babu wanda ya taba zuwa can ya gani. Idan har kayi rayuwa ta gaskiya, idan ka mutu ranka zai kwanta cikin jin dadi. Idan kuma kayi rayuwar da ta sabawa haka ranka zai kwanta cikin tashin hankali.”

Share this


Author: verified_user

0 komentar: