Friday, 14 February 2020
Ronaldo ya taimakawa Juve da ci 1 a wasan da suka yi 1-1 da AC Milan

Home Ronaldo ya taimakawa Juve da ci 1 a wasan da suka yi 1-1 da AC Milan
Ku Tura A Social Media


Tauraron dan kwallon kafar Juventus, Cristiano Ronaldo ya taimakawa kungiyar tashi ta ci kwallo 1 a wasan da suka buga a daren yau da AC Milan wanda ya kare da sakamakon 1-1.

Wasan zagayen farko na kusa dana karshe na cin kofin Coppa Italiya an tafi hutun rabin lokaci ba tare sa cin kwallo daga kowane bangare ba.

Bayan dawowa daga hutun rabin lokacine, Milan ta saka kwallo 1 wadda ta makale. Ana mintin karshe na wasa, Ronaldo ya so ya ci kwallon ban mamaki da watsewa amma bai yi nasara ba.

A nanne na'urar VAR ta baiwa Juve bugun daga kai sai gola wanda Ronaldo ya ci mata. A yanzu Ronaldo na da kwallaye 12 a wasanni 8 daya buga a shwkarar 2020.

An dai yi cece-kuce sosai akan bugun daga kai sai me tsaron gidan da aka baiwa Juve.

Share this


Author: verified_user

0 komentar: