Friday, 14 February 2020
Wata Mata Tayi Yunkurin Rigon Allah Ga Ran Kishiyarta

Home Wata Mata Tayi Yunkurin Rigon Allah Ga Ran Kishiyarta
Ku Tura A Social Media

Rundunar ‘Yan sandan jihar Kano, ta kama wata mata mai suna Sa’adatu Umar ‘yar kimanin shekaru 28 da a ke zargin ta kwarawa kishiyar ta tafashashshen ruwanzafi a Kano.

Lamarin dai ya faru ne a unguwar Kofar Waika dake karamar hukumar Gwale a birnin Kano.

Matar Sa’adatu Umar, a na dai zargin ta ne da watsawa abokiyar zamanta Zuwaira Umar mai shekaru 28, tafashashshen ruwan zafi a kafada wanda hakan ya yi sanadiyar salibewar kafadar ta.

Da yake zantawa da wakilin mu, kakakin rundunar ‘Yan sandan, DSP Abdullahi Haruna, ya bayyana cewar bincikensu ya tabbatar da cewar Uwargidan Mai suna Sa’adatu Umar, ita ce ta kona Amarya Zuwaira Umar da ruwan zafi domin haka suka gurfanar da ita a gaban kotun.

Wakilin mu Abba Isah Muhammad, ya rawaito cewa mai magana da yawun rundunar ‘Yan sandan na Kano, DSP Abdullahi Haruna, ya kuma gargadi sauran jama’a wajen kaucewa daukar doka a hannu Musamman ma Ma’aurata domin kaucewar dana’sani.

Share this


Author: verified_user

0 komentar: